Ataba Husainiyya ta bude sabin Ajujuwa a fannin kimiya da kiwon lafiya

Jiya Laraba 7 ga watan Disamba 2022 Ministan Ilimi ta koli Dakta Na’eem Abudi ya bayyana irin taka Rawan gani da Haramin Imam Husain (as) take yi wajen bude ayyukan kimiyya da likitanci a Karbala da kuma wasu Kananar hukumomin Iraki, ajiyan Wakilin Marji’iyya kuma Shugaban gudanarwa na Harami Shaik Abdul Mahdi Alkarbala’i ya samu halatar bude sabon wajen tare da halartan Gwomnan Karbala hadi da wasu Wakilan Jihohin na Ilimi 

 Ya kara da cewa Hukumar kula da lafiya da Ilimi na Haramin Imam Husain sun fitar da sanarwa bude wasu sababbin sassa a Jimi’ar Azzahra na mata na tantance kworarrun likitoci 

 Abin lura acikin Maganar ministan Ilimi a wajen taron wasika ce na cewa ya kamata cibiyoyin Ilimi masu zaman kansu su dauki wannan matakin su zama Kamar Jami’atu Zahra na mata tare da samar da dukkanin hanyoyi ci gaba wanda zai in ganta Dalibai domin inganta Ilimi a kasar Iraki 

 Ya kara da cewa ilimi na Gwomnati da masu zaman kan su zai kasance a kan hanya guda daya ne, kuma mun shaida da irin taka rawar da Harami Imam Husain takeyi wajen kafa fitattun gine-ginen Kimiyya da na likitanci ga Al’umma Iraki 

 A daya bangare kuma, Shugaban hukumar kula da lafiya da Ilimin likitanci na Hubbaren Imam Husain (as) Dakta Sattar Al-Sa’adiy ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa Wadan nan ayyukan sun hada da na kasa da kasa da fitattun shirye shirye Ilimi da ilimi kuma shine karo na farko a Iraki 

 Ya ci gaba da cewa bude ajujuwa da sassa dakin Gwoje-gwoje na zamani da sauran su duk suna cikin tsarin namu hadi da dukkan bangarori na Ilimi 

 Ministan Ilimi da mai kula da harkokin Harami Shaik Abdul mahdi karbala’i sun bude dakin karatun na Jami’atul Zahra (as) tare da duba dakunan gwoje gwoje na musamman da suka shafi har hada maguna da likitanci da fasaha

abubuwan da aka makala