Sama da Gidaje (509) Ataba Husainiyya ta ginawa Marasa Galihu a Yankin Karbala

Ɓangaren Kimiyya da fasaha Na Haramin Imam Husain (AS) na ci Gaba da aikin Samar da Gidaje ga Marasa ƙarfi a Yankin Ibrahimiyya da ke kudu maso Gabashin karbala .

 Injiniya Muhammad Hasan Tamimi ya bayyana haka ne a wata Hira da kafar sadarwa na yanar Gizo, inda yake cewa karkashin Umarnin Wakilin Marji’iyya kuma Babban Mai kula da Haramin Imam Husain (AS) Shaikh Abdul Mahdi karbala’i yayi Umarni ga ma’aikatan da su cigaba da samar da aikin gina Gidaje ga Marasa ƙarfin yankin Ibrahimiyya, saboda aikin kulawa da marasa Galihu na ɗaya daga cikin manyan Ayyukan Haramin Imam Husain (as).

 Ya kara da cewa an tsara aikin Ginin ne akan Yalwataccen ƙasa wacce faɗin ta yakai (150) tare da tsara gina gidaje (509) inda ya bayyana cewa an ware gina Benayen a tsakanin mita 120 zuwa 150 .

 Acikin Maganar sa ya kara da cewa aikin ya hada da makarantu 4 na mata da maza hadi da wajen renon yara tare da da Asibiti, masallaci da kasuwa .

 Altamimi yayi nuni da cewa an kuma kafa cibiyar kula da ruwan sama dana tsaftace muhalli hadi da wutar lantarki da Tituna da wurin shakatawa.

abubuwan da aka makala