Ataba Husainiyya ta sanar da cigaba da bibiyar lafiyar wani Maziyarcin Imam Husain (AS) dan K'asar Bahrain da yin masa Jinya kyauta bayan ya kamu da rashin lafiya mai tsanani a Asibitin ƙwararru na Imam Zainul Abidin (AS) wacce take ƙarƙashin kulawar Haramin bisa Umarnin Wakilin Babban Marji'i Addini Shaikh Abdul Mahdi Karbala'i,
Mai magana da yawun Wakilin Haramin a Harkan lafiya Fadil Auz ya bayyana a wata Hira da yayi da kafar yanar Gizon Hukuma cewa; mun samu kira daga Wani Ma'aikacin Haramin Imam Husain (as) kan wani maziyarci dan kasar Bahrain da Allah ya Jarabta da rashin lafiya kuma yana Bukatan kulawa sosai.
ya kara da cewa an binciki lafiyar bisa kulawar tawagar ƙwararrun likitoci kuma yanayin lafiyar sa yana daidaita, Albarkacin Manzo da iyalan gidan sa da kuma kokarin fitattun Ma'aikatan lafiya na Asibitin.
ya ci gaba da cewa Limamin Haramin Imam Husain kuma Wakilin Marji'i na Addini Shaikh Abdul Mahdi ya ya bada Umarni da abi diddigin halin da Marar lafiyar ke ciki ya kuma Umarci da a bashi kulawa ta musamman tare da kebe shi da girmamawa sannan ya haɗa da sakon gaisuwa gare shi Kasancewar sa Maziyarcin Imam Husain (AS) .
اترك تعليق