Bayan fitar da fatawar Jihadin kare kai daga mamayan 'Yan Da'ish da Babban Marji'in Ƙasar Iraqi ya bayar a watan Yuni na 2014 ne wasu gungun Mutane suka ƙirkiri wani tsarin asusu da suka bashi suna ''Akwatin Gidajen Shahidai'' inda suka samar da akwatin a tare da kallafawa kansu ajiye kuɗin da ƙimarsa ya kai Naira dubu uku da ɗari. Tunanin haka ya samo asali ne bayan da suka kai ziyara ga Iyalan Shahidai a Garin Ramsiyya dake Yankin Musannah inda suka samu wasu 'ya'ya shida daga cikin Iyalan Shahidai da suke rayuwa a cikin Bukka ɗaya. Sun bayyana cewa bayan Ɗan Gajeren lokaci yawan masu wannan alkawari ya cigaba da fadada inda ya zuwa yanzu sun iya samar da gidaje sama da 300 a Garuruwa mabanbanta na Iraqi, haka nan shima akwatin an Fadada ayyukansa zuwa Garuruwa.
اترك تعليق