SABON FARFAJIYAR ƘARƘASHIN ƘASA DOMIN ƘARƁAR MAZIYARTA IMAM HUSAIN DA KUMA SAMAR MASU DA WALWALA.

 

 Ɓangaren kula da aikin Gine-gine da fasaha na Haramin Imam Husain dake Karbala  ya ayyana lokacin buɗe Sabbin Gine-ginen ƙarƙashin ƙasa har guda hudu da aka samar a cikin Haramin.      Shugaban Ɓangaren, Injiniya Husain Ridha Mahdi, Ya fadi hakan ne a yayin Zantawa da kafofin sadarwa ta musamman cewa; "Haramin na Imam Husain tana aiki tukuru domin haɗe sabbin gine-ginen Ƙarƙashin ƙasa hudu da aka samar, don ganin sun fara aiki nan bada jimawa ba, "  inda yace " Ranar buɗewa ta Musamman ɗin zai zai kasance ne kafin Ranar Arba'in mai zuwa.       Sannan ya kara da cewa "jimlar Girman wa'yannan gine-ginen ƙarƙashin ƙasar sun kai (adadin murabba'in mita dubu hudu),"      Inda ya kara bayyana cewa ; munufar hakan shine taimakawa wajen karbar ƙarin Adadin Maziyarta masu yawa, Musamman ma a kwanakin da miliyoyi ke tunkudowa zuwa Ziyara.

abubuwan da aka makala