Cibiyar karatu Al- qur'ani karkashin Haramin Imam Husain sun gudanar da taron Yiwa falastinawa Addu'a

Cibiyar karatun Alqur'ani karkashin Jagorancin Haramin Imam Husain mai Alfarma na Sanar da Taro don karanta Qur'ani izuwa ga Ruhin Shahidai falastinu, inda zai samu halartar Wasu daga fitattu Makaranta na wasu kasar       Daya daga cikin masu kula da Shashin Qur'anin Husain Shaikh Hasan Mansuri ya fada a wata hira da yayi da kafar yanar Gizon Hukuma cewa: an gudanar da taron ne a matsayin Jinkai ga Rayukan Shahidai masu Girma Wanda suka bada kariya ga Masallacin Qudus Mai Tsarki da kuma yan Gwagwarmaya na palastin akan masu musu mamaya       Ya bayyana cewa an gudanar da taron ne na kasa da kasa tare da hadin gwiwar shahen yada labarai na Haramin Imam Husain (as) tare da dandalin sadarwa na zumunta da wasu manya  Halarta  kuma fitattu Makaranta wadanda ke wakiltar Iraki da kuma sauran Kasashen Musulmai       Ya ci gaba da cewa kasashen Musulmai da suka Halarci taron sun samu Wakilcin Indunisiya Iran da Lebanon, yana mai cewa  wannan matsayin na hadin kai yana nuna Ruhin Imani ne da kuma Matsayi da Alfarma na Alkibla Musulmai ta farko a tsakanin Musulmai na ko'ina a Duniya       A nasa bangaren Yasir Al_Talqani, Mataimakin Daraktan Gidauniyar Haramin Imam Husain  (as) na bangaren yada labaran Harami ya ce: taron ya guda ne daidai karfe takwas na yamma Ranar Talata, mayu,23,2021   Yace Dandali su na sadarwa sun dauki taron kai tsaye kuma sun kammala dukkan kayan aikin su      Abin lura anan shi ne shashin karatu Qur'ani na Harami yana maida Hankali sosai kan ayyukan da ya shafi Alkur'ani mai Tsarki a kowane nau'i kuma a matakin Iraki da kasashen Musulunci haka kuma yana daya daga cikin bangarorin da ke da niyyar kafa tsararrun Al_kur'ani masu dauke da koyarwar Allah   Kuna iya bibiyan shashin Bangaren Qur'ani ta wannan link din dake kasa   http://t.ly/91AH

abubuwan da aka makala