Haramin Imam Husain ta fara Gina makarantu ga marayu a cikin garin Karbala

Haranin Imam Husain mai Alfarma ta sanar da soma ci gaba da aikin gina makarantu na marayu a garin karbala       Injiniyan aikin Zaid Azzam,ya fada a wata hira da yayi da gidan Yanar Gizon Hukuma cewa:aikin yana daya daga cikin manya muhimman Abubauwa da Harami ke aiwatarwa ga marayu, karkashin kulawan bangaren injiniyoyi da masu Fasaha.  aikin ana aiwatar da shine a wani fili wanda yakai tazara 10 daga kwaryan Garin Karbala a unguwan salam       Ya ci gaba da cewa yanzu haka matakin ayyukan yakai kashi  (50) kuma ya hada da Makarantu shida guda uku na Maza guda uku (3) na Mata sannan Makarantu ya hada Firamari ne da sekandari hadi da wajen renon Yara tare da wajen wasanni  da Asibitin Kiwon Lafiya,ya sake tabbatarwa  cewa dukka ayyukan nan anayin su ne a kyauta 

abubuwan da aka makala