Shugaban Ɓangaren Kwana kwana na Haramin Imam Husain AS dake Karbala Husain Muhmiy ya sanar da Nasarar da Ɓangaren nasu ya samu ta hanyar iya samar da kayan aiki da na'ura da kan iya gano inda gobara ta taso da kuma Musabbabinta tare da iya kawar dashi cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan cigaba dai yana samuwa bisa karfafawan Wakilin Babban Marji'in Ƙasar kuma wanda Shine Babban Mai jinyarta lamurran addini a Haramin wato Sheikh Abdul Mahdy Al Karbala'i Dz. An rarraba wa'yannan kayayyakin zuwa manyan ƙofofin shiga Haramin domin jiran ko ta kwana, musamman a daidai wannan lokaci na tsananin zafi. Ita wannan Shashi na kwana kwana tana gudana da ayyukansa cikin Harami da kuma sauran Sassa na Garin karbala tare da Haɗin Gwiwa da Ma'aikatar Hukumar kwana kwana na Garin karbala Mai Tsarki.
اترك تعليق