An kewaye Haramin Imam Husain da inji mai sana'anta kayayyakin kariya da riga kafi domin taimakawa Maziyarta da Takunkumi da Man tsaftace Hannu.

Bisa dacewa da Ranakun tunawa da  shahadar Imam Husain (as) Masana'antar Raihanatul Waris dake ƙarƙashin Haramin Imam Husain Mai Tsarki ta samar da Injinan feshi mai Sarrafa kansa a kewayen Haramin da kuma wurare da dama a cikin Gari da ma wasu Garuruwa hadi da raba  Takunkumin fuska  don kariya daga kwayar Cutar Korona .   Daraktan  Ma'aikatan Abdulsahib Adnan a cikin wata hira da yayi da yanar Gizo yace: ma'aikatar Raihantul Waris da ke ƙarƙashin Haramin ta tattara Membobin ta domin taimakawa Maziyarta wajen kula da lafiyar su ta hanyar sanya Injinan feshi mai Sarrafa kan Shi a duk kewayen Haramin Imam din da kuma cikin garin tare da ajiye masu Raba Magunguna da kuma Abubawan kashe Gobara hadi da Takunkumi Fuska ga Wanda zai shiga karbala .     Yaci gaba da cewa kungiyar namu ta samar da masu wayar da  kan Maziyarta  ta hanyar sanar da su Mahimmancin saka takunkumin Fuska da kuma aiki da kayan wanke Hannu akai akai .      Yayi karin haske cewa Ma'aikata na cigaba da bada kariya a kewayen Haramin Imam Husain (as) da kuma cikin Haramin .   An bada Rahoton cewa Raihanatul Waris da ke karkashin HaraminImam Husain tana samar da sinadari kala kala tun farkon fara  yaduwar cutar korona.

abubuwan da aka makala