An gabatar da Majalisin Tunawa da Ranar da Áli Sa'ud suka Ruguza Makabartar nan ta Jannatu Baki'a dake Madina, wajen da ya tattara da yawa daga Iyalan Annabi S ciki har da Imam Hasan Almujtaba , Imam Bakir, Imam Zainul Abidin, Imam Sadiq (AS) da Sauran Bayin Allah Nagargaru. Wannan Ta'addanci dai ya auku ne ranar 8 ga watan Shawwal bisa Jagorancin Gidan Sarautar Ali S'aud dake goyon bayan Aqiidadat Wahabiyyanci. Majalisin ya gudana ne a cikin Haramin Imam Husain dake Karbala Iraqi.
اترك تعليق