Kamfani Ayyuka Ginin karkashin kasa na Haramin Imam Husain mai girma ya sanar da fara ci gaba da aikin hadewa tare da fadada Haramin ta cikin ƙarƙashin ƙasa na tsawan mitoci masu yawa. Mai kula da aikin, Injiniya Salam Sa'aduni, ya fada a cikin hira da tashar yanar gizon hukuma, cewa "Injiniyoyi da masana fasaha suna ci gaba da gudanar da aikin ginin ƙarƙashin ƙasa kuma zasu haɗe shi ne tare da faɗaɗa Shi zuwa Al-Ha'ir Al-Hussainiy." Ya bayyana cewa "yanzu ana aikin ne daga karkashin wata kofar shiga Haramin da ake kira kofar karama da take a gefen arewacin hubbaren Imam Hussein (As) aikin haɗin, ana faɗaɗa ƙofar daga (mita 2.5) zuwa ƙari fiye da (mita 7). " Ya kara da cewa "za'aci ci gaba da kokari na aikin kuma za'a kaddamar da bude aikin a watan Muharram . A cikin Jawabin nashi yake cewa , "ita wannan kofar ta karama ɗaya ce daga cikin ƙofofin da ake fita da gudu sarsarfa a Ranar Ashura don haka ne za'a kara fadada shi. Ya ƙara nuni da cewa "za a kawata kofar da Kashi Karbala'i mai kyau, gilashi da rubuce rubucen Musulunci da kuma zane zane wadanda suka dace da girmamawa na tsofaffin tarihi da kuma tarihin wurin." Abin lura shi ne cewa Hubbaren Imam Husaini mai tsarki ya dauko wani shiri na fadada hubbaren Imam Hussain (As) ta hanyar aiwatar da shimfidar kasa da farfajiyar da ke kewaye da ita, har da farfajiyar Aqeelah Zainab (as) wanda ana aiwatar da shi a kan murabba'in mita dubu (150).
اترك تعليق