Bisa dacewa da kusantowar lokacin jarabawar Kammala karatun 'Yan Aji shida na Sakandare, Cibiyar Annurul Husain wacce take karkashi Haramin Imam Husain (as) ta samarwa da Kwararrun Malamai a fanni daban daban don yiwa yaran daura kyauta tare da daukar takalifin Hidimar Jigilarsu.
Daraktan cibiyar Khidir Mukthar ya bayyana a wata Hira da yayi da shafin yanar gizo, inda ya ce cibiyar ta Annurul Husain (as) tana gudanar da dimbin ayyuka ga Dalibai kasancewar a yanzu haka tana gudanar da kwasa_ kwasan ga daliban Wanda suka hada mata da maza anan cikin garin Karbala mai Tsarki.
Ya kara da cewa kwasa-kwasan ana yine da manufar karfafa tunanin Dalibai da kuma taimaka musu wajen cin Jarabawan karshe na sakandare cikin nasara .Kasantuwar Wadannan Darrusa wasu Mutane ne kwarraru na musamman ke koyar.
Ya kara da cewa Darussan zai cigaba ne a cikin kwanakin mako kuma an samar da Abun hawa don Jigilar Daliban na zuwa da dawowa daga cibiyar zuwa duk wani unguwa dake birnin Karbala.
اترك تعليق