A Ƙarkashin kulawar Wakilin Babban Marji'in Iraqi Haramin Imam Husain (as) sun karbi Baƙuncin Ɗalibai 100 Wanda sukayi Rijista kyauta a karatun Daura da aka shirya masu. Mai sa ido kan Dauran Sheikh Amir Al-wali a yayin hira da akayi da shi ta yanar Gizo yace Ƙarƙashin Mai kula da lamurran Addini na Haramin wato Sheikh Abdul mahdi Al-karbala'i da kuma wanda ke kula da makarantun Addini Yace an Bude Dauran ne don ci gaba da karatu ga wa'yanda suka kammala karatunsu na Sakandare. Sannan Ya kara da cewa akalla Ɗalibai dari ne tsakanin maza da mata wa'yanda suka aka koyar dasu Darussa da suka haɗa da ilmin lissafi,Turanci,da kuma fasaha. ƙwarrarun farfesosi ne dai aka zaba wanda suka haɗa da Muhammad Nazir, Ferfesa Haidar Abbas Jumal wato malamin da ke koyar da yaran Turanci da kuma Farfesa Muthanna Muhammmad Al-Mawla Malami a fanni Fasaha da Farfesa Husaini Mahdi Al- sharifi Malami kan fanni lissafi a Mataki , sai kuma malami ɓangaren Kimiyya wato Abdullah Al-shabawi.
اترك تعليق