MASANA'ANTAR DAKE ƘARƘASHIN HARAMIN IMAM HUSAIN TA FARA SANA'ANTA KAYAYYAKIN ƊAKI NA ZAMANI KWATANKWACIN WANDA AKE SHIGOWA DASU DAGA WAJE

A Ƙoƙarinta na bunƙasa kayan da ake samar dashi a Gida da kuma samar wa da Matasa guraben aikin yi,  Hubbaren Imam Husain ta sanar da samar da Masana'antar "Ataa al warith" wanda ke sana'anta kayayyakin adon Ɗaki na Zamani.      Daraktan Gamayyar Masana'antar, Iskandar Shamsi, ya bayyana  hakan a yayin Zantawa da Gidan Talabijin ɗin Karbala cewa;  a karkashin Babban sakatariyar Haramin Imam Husain Masana'antar Alwarith ta shirya tsaf domin Samar da kayayyakin Ɗaki na Zamani don isarwa izuwa kasuwannin cikin Gida, wa'yanda kuma sune irinsu na farko da aka sana'anta su a Iraƙi.      Haka nan ya kara da cewa "an tanadar wa da Masana'antar injina  na zamani"  yayinda kuma masana'antar an gina shine a faɗin Murabba'in mita dubu 25, kuma shine irinsa na farko a Iraƙi dake samar da Gadajen Zamani, Kujerun Ɗaki da kuma kayayyakin Ofis.        A nashi ɓangaren, Babban mai sa Ido akan abubuwa da ake Sana'anta, Waseem Al-Saadi, Yace ; Abubuwan da Masana'antar ke samarwa a kullum ya doshi Gadaje aƙalla 30 zuwa 50.        Ita dai Haramin Imam Husain dake Karbala bisa shiryatarwar Wakilin Babban Marji'in Ƙasa kuma Mai kula da lamurran addini a Haramin, Sheikh Abdul Mahdi karbala'i (Dz)  a ƙarƙashin ƙasa tana aiki tukuru don inganta tattalin Arzikin Iraƙi , Sawa'un ta hanyar kayayyakin da take samarwa ne da aka bashi Taken (Made in Iraq) ko kuma ta hanyar samar da aikin yi ga Matasa, tare da samar wa da kasuwannin cikin Gida kayayyaki masu inganci domin shigar da natsuwa a zukatan al'umma.

abubuwan da aka makala