Shin kana Kwadayin ka zama daya daga cikin Maziyarta Abul Fadalul Abbas (as) sanya sunanka domin amaka ziyara acikin Haramin sa a maimakon ka

Mu'assasar Imam Husain AS  mai yaɗa labarai a kafofin sadarwa Yanar gizo karkashin Haramin Imam Husain AS ta shirya gabatar da Ziyara ta musamman  a ranar Litini bakwai ga watan Muharram Wanda yayi daidai ga 16/8/2021   Ka shiga wannan link din dake kasa don sanya sunan ka  https://www.imamhussain.org/hausa/enaba

Daraktan  Mu'assasan Wala'i Safariy yace: za'a Gudanar da ziyarar Abul Fadalil Abbas  (as) ranar bakwai ga watan Muharram mai Alfarma Amadadin Masoya Ahlul Baita  (as) wadanda suka sanya sunayen su a shafin nan namu na ziyara ta Haramin Imam Husain  (as)

Ya kara da cewa miliyoyin masoya Ahlul Bait ne daga sassa daban daban na Duniya suke son kawo ziyara ga Imam Husain  da kuma Dan'uwan sa Abdul Fadal Abbas, amma haka mai wuya ne kasantuwa barkewa kwayar cutar Korona 

 Ya ci gaba da cewa wannan shafin ta samar da wani shiri mai karfi don tattara sunayen wadan da ke zuwa shafin ta suna saka sunan su domin a mu su ziyara a madadin su

 

abubuwan da aka makala