Limamin Haramin Imam Husain yayi Umarni da ayiwa mutane jinya kyauta a Asibitin Zainul Abiden don murna zagayon Fiyayyen halitta (saw)

Limamin Haramin Imam Husain (as) kuma Wakilin babbar Marji' na kasar Iraq Shaik Abdul Mahdi karbla'i yayi Umarni ga Asibiti Zainul Abiden da ke karshin Haramin Imam Husain [as] yiwa mutane Jinya kyauta, don murnar zagayowar haifuwar fiyayyen halitta

 Shugaban Hukuma kula da lafiya na Haramin Imam Husain Dr Sattar Al-asa'adi acikin wata hira da yayi da yanar gizon Hukuma ya ce: a karkashin jagorancin Wakilin babban malamin addini kuma mai kula da Haramin Imam Husain (as) Shaik Abdul Mahdi karbala'i ya kaddamar da wani sabon shiri a matsayin ayyuka na jin kai ya bada umarni da ayiwa mutane jinya don girmama watan haihuwar Annabi Rahma Muhammad (saw) da Jikar sa Imam Ja'afar Sadiq na shida daga cikin Imamai Shari'a Aminci Allah ya tabbata a gare su 

shugaban Hukuma kula da lafiyar acikin jawaban sa Yayi bayani cewa Asibitin Zainul Abiden (as) yayi shiri na musamman don Karban Marasa lafiya maza da mata saboda yi mu su jinya kyauta tin daga Ranar 12 ga Rabi'ul Auwal 19 ga oktoba

har zuwa 17 ga Rabi'ul Auwal 24 ga watan oktobo 2021 na tsawon kwanaki biyar kenan

domin neman bayani kana iya kiran mu a wannan lambar

07725986480

Tarjama

sayyid Adam Njubulwa

abubuwan da aka makala