Ana kanyiwa mutane (215) Tiyata kyauta don Murnan zagayon Haihuwar fiyayye Halitta (saw)

A Makon Tunawa da zagoyawar haihuwar fiyayyen Halitta Manzo Rahma Muhamamd dan Abdallah (S.A.W) da jikan sa Imam Ja'afar Sadiq (A.S) na shida daga cikin Imamai Shari'a, Haramin Imam Husain taci gaba da yiwa mutane jinya kyauta da kula da marasa lafiya don Girmama watan haihuwar fiyayye Halitta annabi Rahma Muhamamd (saw) a karkashin,Jagorancin Wakilin babban Malamin addini Shaik Abdul-Mahdi karbal'i 

 Daraktan Asibitin Dr Maisan Ashar'i ya bayyana a wata hira da yayi da yanar Gizon Hukuma cewa: da Umarnin limamin Haramin Imam Husain (AS) ne na cewa ayiwa mutane jinya kyauta a cikin Wannan kwanaki na murna da haihuwar Manzo Allah (saw), Kuma Asibitin ta karbi mutane masu adadi mai yawa daga cikin dukkanin Garuruwan Iraki 

 Ya kara da cewa an kara kwanaki da akace an kididdige sakamakon yawan marasa lafiya da suka halarci Asibitin domin wadanda za'yiwa aikin tiyata kadai sunkai (215) 

 Abin lura de shine ita Haramin Imam Husain karkashin Jagorancin babban Malami na addini Shaik karbal'i ya dauki matakai masu kwari wajen ganin ayiwa Al'ummar Iraki masu dimbin yawa d jinya kyuata musamman ma Jami'an Tsaron da aka fafata da su wajen bada kariya a yayin jihadi kare kai da kuma gajiyayyu da  yayan Shahidai da marayu

abubuwan da aka makala