Haramin Imam Hussain ta bada manya motoci da kanana guda (338) don Jigilar baki maziyarta Imam Hussain a Arba'in kyauta

Shashin Jigila na Haramin Imam Hussain ta sanar da kebe motoci don jigilar Maziyarta Arba'in zuwa garuruwa kafin da kuma bayan taron  Arbaeen.

 Shugaban sashen, kula da motocin Harmin Adil Al-musawiy ,ya fada a cikin wata hira da yayi da gidan yanar gizon hukuma, cewa "a karkashin jagorancin wakilin babban malamin addini, kuma mai kula da Haramin Imam Hussain Sheikh Abdul Mahdi Al-Karbalai. , yace shashin jigalar ta ware dukkan ƙafafun ta don jigilar baƙi. "

 Ya bayyana cewa “sashin, ayayin ziyarar arba’in, ya bada mota makafolo sama da (150) da coaster (85) da bos, (62) hadi da motocin da ake musu chaji, (11) da motar asibiti, da  mashinan ruwa don jigilar baƙi. .

 Ya kara da cewa shirin sashen ya hada da safarar baki kafin, lokacin ziyara da kuma bayan kammala ziyarar Arba'in

 yana mai nuni da cewa bayan kammala bukukuwan ziyarar, sashen ya tabbatar da zai kai maziyartan garuwan kamar Babilon karbala da sauran su 

 Ya kara da cewa sashin ta ware motocin yayin ziyarar arba'in (338) duk don jigilar maziyarta ne (kyauta).

 Yana da kyau a lura cewa ita  Haramin Imam Husain tanayin amfani da dukkan sassanta da ma’aikatanta, kamar kiwon lafiya, asibitoci da hidimomi, masaukin baƙi,da masana’antar ƙanƙara, da sauransu, don hidimar baƙi a duk lokutan taruka na musamman da lokutan ziyarar arba'in na Imam Husaini (a.s).

Tarjama

Sayyid Adam Jubulwa

abubuwan da aka makala