Jerin gwano kusan (11356) za suyi musharaka bana don shiga Harami Hussain a ranar Arba'een

Sashen lura da masu jerin gwano (maukibobi) na Iraki da duniya musulunci wacce take karkashin Haramin Imam Hussain da Abul fadal Abbas  , sun bayyana adadin Jerin gwanon da za su shiga cikin Harami a kwanakin Arba'in na Imam Hussain (as) sannan shashin ta jaddada kiyaye ka'idoji don lura da lafiya 

 Shugaban shashin Riyat Na'im salman, ya fada a wata hira da yayi da yanar gizon Hukuma cewa tun ranar Ashirin da biyar ga watan Muharram shashen kula da jerin gwano na Harami ya bada tabbaci cewa masu jerin gwano za su shiga Harami kamar yadda aka saba duk shekara 

 Ya kara da cewa yanzu haka sama da maukibobi (11356) daga cikin Iraki hadi da wa su kashen larabawa dama wadanda ba larabawa ba (59) suka bada sunan su domin shiga Haramin kamar su (china, sudan, Saudiyya Siriya, Iran labnon pakistan, Indiya Nigeria kenya, da sauran su ) wanda da suka sajjala domin shiga Harami Imam Husain (as) a ranar Arba'een bugu da kari kuma za'a samarwa Al'umma abubuwa kulawa 

 Ya kara da cewa Jerin gwonon (maukibobin) da suke girki za'a samar mu su da gass na girki da sauran kaya da su ruwan sha kyauta 

Bayan ga umarni da limamin Harami ya bamu da anemawa Al'umma ma'aikata kiwon lafiya da lura da jerin gwanon da sharudan Rigakafi da takunkumin fuska da kuma warware jama'a don hana cinkoso 

 Yana da kyau a lura cewa shashen kula da jerin gwano (maukibobi) na Iraki da Duniya musulunci gaba daya wacce take karkashin Haramin Imam Hussain (as) suna aiki kan tsara ayyukan shigan miliyoyin mutane cikin Harami da kuma samawa mutane wurare hutu da kwana yayin Ziyara na Arba'een

abubuwan da aka makala