Limamin Haramin Imam Husain ya bada umarnin fitar da miliyan 100 don yiwa Mutane 13 Jinya

Wakilin babban Marji'i Na Iraq kuma limamin Haramin Imam Husain, shaik Abdul-Mahdi Karbala'i: yayi umar da yiwa mutane 13 jinya a Jihohi hudu da ke cikin kasar Iraki 

  Mataimakin shashen kula da Iyalan shahidai da Maraunata na Haramin Imam Husain Ahmad kafaji ayayin Hirar sa da wata gidan yanar gizo Hukuma ya ce: Limamin Harami yayi umarni da kula da mutane 13 da za'ayiwa tiyatan Dashen oda da kashi da kuma ciwon Siga majinyatan suna Jihohi hudu ne (Wasid misan karbala Bagadaza,) 

 Ya kara da cewa bayanin Rubutun Shaik Abdul-mahdi din yana nuni da cewa Ofishin babban Marji'i na Iraki itace zata dauke nauyin Jinyar kuma ta fitar da miliyan 100 domin kula da majinyatar 

 Yaci gaba da cewa jinyar mutum 13 zai kasance ne ga mutane garuwan nan (6 daga jihar wasid hudu daga jihar karbala 2 kuma daga Jihar bagadaza sai kuma daya garin misan) 

 Abin lura shine Haramin Imam Husain (as) ya na maida hankali sosai wajen yiwa mutane Hidima jinya, musamman ga mutanen da ke fama da cututtukan da ba su da magani, kamar yadda Asibitin Zainul Abidin (as) ta gudanar da ayyuka kyauta a kwanakin baya wacce itama tana karkashin kulawar Haramin Imam Husain (as) ne

abubuwan da aka makala