A yayinda yake zantawa da kafofin sadarwa, Sakataren Musamman na Hubbaren, Abbas Ƙaim ya sanar da isowar kyautar ƙofofin hudu na Zinare daga wasu Bayin Allah Masoya Iyalan Annabi S daga Ƙasashe Mabanbanta na duniya zuwa ga Hubbaren. Ya ƙara da cewa; "ƙofofin guda hudu za'a sanya su ne a wurare na musamman dake cikin Hubbaren, inda za'a sanya masu sunaye daga cikin Sunayen Iyalan Annabi S, Ɗaya daga ciki zai amsa sunan ƙofar Imam Ali inda za'a sanya shi a ƙofar dake fuskantar Cikin Hubbaren, sai kuma ƙofar Imam Hassan Al-Mujtaba, da kuma Ƙofar Imam Husain AS inda za'a sanya su a hanyar wucewa na Maza zuwa cikin Hubbaren". Cikon na huɗun da aka sanya wa sunan Sayyida Zainab AS, za'a sanya shi ne a ƙofar shigowar Mata dake cikin Hubbaren mai tsarki. Bukin ƙarbar ƙofofin dai ya samu halartar mutane mabanbanta daga Al'umma, kama daga ma'aikatar Haramin da jami'an ma'aikatar Shari'a na ƙasa da kuma Shuwagabannin Ƙabilu. Shi dai Sayyid Muhammad Ɗane ga Imam Aliyul Hadi AS kuma Ɗan uwa ga Imam Askariy AS, ya kasance Ma'abucin Ilmi da karamomi masu yawa, saboda baiwar da Allah yayi masa wasu har sun ɗauka shine zai gaji matsayin Imamancin Mahaifinsa, an rawaito cewa yayi shahada ne a Garin Balad kilomita 50 tsakaninsa da Samarra, yayin da yake hanyar komawa Madina bayan ya ziyarci Mahaifinsa Imam Hadi.
اترك تعليق