HARAMIN IMAM HUSAIN YA BAYAR DA KYAUTAR LITTAFAI DA WASU KAYAYYAKI GA KWALEJIN KOYAN AIKIN JARIDA NA JAMI'AR IRAQI

     Daraktan aikin  yaɗa labarai na Haramin Mai Alfarma,   Ali Shubur ya faɗa a yayin Zantawa da kafofin sadarwar yanar Gizon Hukuma cewa; A karkashin kulawar Sheikh Abdul-Mahdy Al-Karbala'i wanda yake shine Wakilin Babban Marji'in ƙasar kuma Mai kula da Harkokin Shari'a na Haramin Imam Husain, an Ziyarci Jami'ar Iraƙi tare da gabatar Mata da wasu littattafai na Musamman da suka shafi fanni Aikin Yaɗa labarai bayan ƙona  Ɗakin Karatu na Jami'ar da akayi a satumbar 2020.       A yayinda yake tsokaci, Shugaban Kwalejin aikin Jarida na Jami'ar, Dakta Ithar Tariq Al-Ubaidi Yace; Haramin ta miƙa masu tarin littattafai a matsayin gudunmawa domin gyara Ɗakin Karatu na Tsangayar yaɗa labarai ta Jami'ar.        Abin lura dai shine ita Haramin ta Imam Husain mai Alfarma ta hanyar Wakilin Babbar Marji'in ƙasar, Sheikh Abdul-Mahdy Al-Karbala'i, a fili  Yake yadda suke bada gudummawa wajen samar da ayyukan yi ga al'ummar Iraƙi da kuma wasu ƙarin Muhimman ɓangarori na bunƙasa ilmi.

abubuwan da aka makala