Wakilin Babban Marji'i na Iraki kuma Limamin Haramin Imam Husain ya Ayyana Ranar Eidil Ghadir ne Za'a bude Mu'asssar nan don kula da masu ciwon kansa kyauta

Babban Wakili Hukuma na Addini kuma Mai kula da Haramin Imam Husain  (as) Shaik Abdul Mahdi Al-karbal'i  yaci gaba da bibiyar ci gaban fara ayyukan masu ciwon kansa kyauta a garin Karbala mai girma       Shugaban sashin kula da Ayyukan na Haramin Imam Husain Injiniya Muhammad Ziya ya ce, Ziyaran Limamin Haramin Imam Husain zuwa wannan Mu'assasa na masu kula da cutikan kansa  don ci gaba da yin jinya masu kansa din ne      Ya bayyana cewa farashin kammala aikin ya kai kashi 98% kuma ranar budewa zata kasance ranar Ghadir ne       Ya kara da cewa aikin ya shiga mataki karshe, ciki kuwa har an sanya kayan daki da aikin zane na karshe       Yaci gaba da cewa wannan aikin na daya daga cikin manyan ayyuka na musamman da suka kware wajen kula da masu cutar daji a cikin Iraki, yana mai nunu da cewa aikin ya kunshi muhimman wurare da kayan aiki na zamani, wasu daga cikin kayan aikin ma sun shigo a Iraki a yanzu haka       Ya jaddada cewa Hubbaren Imam Husain yana mahimmatar da wannan ayyukan don bawa mutane Iraki kulawa       Abin lura shine aikin Gidauniyar wannan Mu'assasa na Haramin Imam Husain  dake kula da cutattukan tayi Shi ne a kusa da tsakiyar gari, wanda masafa sha biyu (12) tsakanin Shi da tsakiyar gari

abubuwan da aka makala