Menene Imam Hussain ke bukata wajenmu bayan kuka da dukan ƙirji..

Wakilin Babban Marji'in Addini har wala yau wanda ke jiɓintar Al'amurar Shari'a na Haramin Imam Hussain Ya fuskantar da Tunatarwarsa  izuwa ga Matasa Mazansu da Matansu da ma Tsoffi da sauran masu Juyayin musibar da ya sami Imam Husain cewa ; Menene Imam ke da bukata a garemu bayan kuka, Juyayi da kuma bugun ƙirji?

 Sheikh Abdul Mahdi Karbala'i yace Imam Husain yana bukata ne daga gare mu baki ɗaya mu ɗauki nauyin Kare wannan gwagwarmaya da yayi mai girma sannan muyi aiki Dare da Rana Domin gyara kawukan mu da Iyalanmu da ma Al'ummar mu sannan kuma mu zama ma'abuta gaskiya a yayin kukanmu da Juyayin mu sannan mu kiyaye Sallolin haɗi da sauran Ibadun mu, muyi ƙoƙarin kiyaye Hakkokin 'Yan'uwan mu, sannan mu kiyaye Hurumin Dukiyoyin Al'umma tare da Kare mutunci.

 Ya kara da cewa:

wannan hawaye da Allah Madaukakin Sarki da Manzonsa da Imam Husain (as) suke so, a lokacin da muke kuka kan laifukan mu, muke nunawa Allah Madaukakin Sarki a fili, da ayyukan mu wajen tsarkake zuciyan mu daga Hassada da hakkoki da girman kai rudu da munafurci

 Yayi nuni da cewa Imam Husain (as) yana so daga gare mu nisanci gaba da Juna da Rarrabuwar kawuka da Abubuwan duniya marasa kan gado da shirme.

 Ya jaddada cewa hakikanin Tarukan Ashura na gaskiya, shi ne mu guji zargin juna da zage zage da fada wajen neman abin Duniya.

 Ya sake cewa karbala Birnin Husain tana son mu farfado da wani farillah wanda yake ɗaya ne daga cikin manya farillai na musulunci, wanda shine raya umarni da kyakkyawa da kuma hani ga aikata mummuna a titunanmu da kasuwanni, makarantu, jami'oi, gidajen mu, Iyalai, da garuruwan mu baki ɗaya.

 Ya ce Imam Husain (as) yana so mu tsarkake kasuwanni mu da mu'amalolin mu daga Haram, Riba Zamba da Rantsuwar ƙarya, kuma muyi kokarin kiyaye Al'adun mu masu kyau da makiya suke son karkatar damu daga gareshi .

 Daga karshe yayi kira ga yan'uwa Mata cewa ya ku masu Juyayi da wannan musiba da ta samu Imam Husain ku sani karbala Birnin Imam Husain (as) tana so daga gare ku da ku kiyaye Hijabinku da sutura haɗe da kamewa cikin ayyuka, Suruta da shigarku, ku kiyaye bayyana Adon da aka haramta maku, ku zama masu nasiha da hani ga mummuna tare da umarni da kyakkyawa Domin ku zama daga cikin mataimaka Imam Husain (as).