Sanya Sunanka Domin Ayi ma ziyara a Haramin Imam Husain a madadin ka cikin daren Nisfu sha'aban daren da yafi kowana dare bayan Daren Lailatul Qadari

Mu'assatul Imam Husain {as} wacce ke karkashin kulawar Haramin Imam Husain Aminci Allah ya tabbata a gare shi tana sanar da ku da cewa ta dauki nauyin yin ziyaran Imam Husain a wannan Dare na Nisfu sha'aban da kuma gabatar da dukkan bukatun ku da kuka sajjala zasuyi muku addu'a mai makon ku a daren, saboda haka mai bukata yana iya sanya sunan shi da sunayen wanda yake bukata a wannan link din dake kasa shiga ciki domin sanya sunan ka da wanda kake so tare da anbatan bukatun ka

 https://www.imamhussain.org/hausa/enaba

 An Rawaito cewa daren Nisfu Sha'aban yana da falala sosai, daga Imam Ja'afar sadiq {as} yana cewa an tambayi Imam Baqir {as} akan falalar daren Nisfu sha'aban yace; itace daren da tafi kowace dare bayan Lailatul Qadari, a cikinsa ne Allah yake bayar da falalar sa ga Bayi kuma yake gafarta zunubai, don haka kuyi kokari wajen neman kusanci ga Allah a ciki,  domin Daren ne Allah madaukakin Sarki baya mayarwa mai rokon face ya amsa masa, a Daren ne Allah yamana falala da shi Ahlul bait kamar yadda yayiwa Annabi da lailatul Qadarii 

 don haka ku himmantu da yin Addua'a da yabon Allah madaukakin Sarki a Daren 

 hakanan Ziyaran Imam Husain {as} tana daga cikin mafificiyan Ayyuka a Daren kuma tana wajabta gafarta Zunubai ga wanda yake so yayi hannu da Ruhin Annabawa 124 yayi ziyaran Imam Husain a daren Nisfu Sha'aban 

 Darktan shafin nan namu ya bayyana cewa hadin guiwa da hadimai na Haramin Imam Husain zasu gabatar da ziyaran Imam Husain ga wadanda suka sanya sunayen su anan shafin 

 Ya kara da cewa shafin namu ta hada wani tawage a domun hada sunayen wadanda suka sanya sunan su a wannan shafin domun ambatan sunan kowa a ranar ziyaran kuma zaka iya sanya sunayen duk wanda kaso ko adadi nawa ne 

ya kara da cewa ranar Juma'a shine zai zama ranar da zamu kulle kamar sunayen Mutane 18\03\2022 domun Asabar ne zai zama Ranar Nisfu a kasar Iraki  

 daga karshe yana cewa kowa zai iya rubuta bukun sa da kuma na makusanta domun ayi masa ziyara a ranar

Tarjama

Sayyid Adam Jubulwa

abubuwan da aka makala