Wakilin Marji'iyya na Iraki , kuma mai kula da haramin Imam Husain Shekh Abdul Mahdi al-Karbalai, ya umurci da a kebe majinyatan da ke dauke da cutar kansa da kuma biya musu dukkan kudaden da masu jinya zasu bukata na sakamakon karbar magani a lokuta daban daban da kuma Abunda ya dace
Sa'ad Al-Din Al-Banna, mamba a kwamitin gudanarwa na Haramin Imam-Husain, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta yanar gizo, inda ya ce wata daga cikin 'yan kasar Iraki wacce ta ke zaune a karamar hukumar Karbala ta kamu da cutar daji, (kansa) inda mai girma Limamin Haramin Imam Husain Shaik Abdul Mahdi yayi Umarni da ayi musu jinya kyauta bisa dacewa da Ranar Haihuwa Sayyida Zainabul Khubra (as) a kwanakin baya wacce jinyar ta ya dauki nauyi mai yawa na magani da sauran su
Ya kara bayyana cewa wakilin mu ya bada umarni dauke mata duk wani nauyi bisa umarnin limamin Haramin
Ya kara da cewa majinyaciyar a sakamakon halin da take ciki na rashin ma'isha an dauke mata dukkan wani abu da suke bukata na daga jinya dama karatun ta sannan kuma an saka mata albashi Albarkacin Ranar Haihuwa Sayyida Zainab
Abin lura anan shi ne ita Haramin Imam Husain
kuma ta hanyar umarnin wakilin hukumar kolin addini, Sheikh Abdul-Mahdi Al-Karbalai, yana ba da hidimar jinya da yawa kyauta ga 'yan kasar Iraki daga dukkan lardunar kasar ,
Haramin takan bada taimakon ne ko dai ta hanyar keber da majinyatar ko kuma a biya musu kudin jinyar akan ƙaddamar ne
Tarjama
Sayyid Adam Njubulwa
a fiye da lokutan bukukuwan Addini na Maulidodi Zuriyar manzo Allah (as) da sauran bukukuwa na Addini .
اترك تعليق