Intifada Sha'abaniyya; Hotunan yadda Saddam ya rugurguza Haramin Imam Husain AS.

A shekarar 1991 ne wanda ya dace da watan Sha'aban Al'ummar Ƙasar Iraqi suka kaddamar da Yunkuri na Musamman don Kawo ƙarshen Gwamnatin Zalunci ta Saddam Husain, Intifadan ya faro ne daga Garin Basrah inda a ƙarshe ya mamaye kusan manyan Garuruwa sha hudu na ƙasar.  A lokacin da Hukumar kama karya ta kasar ta ga alamar za'a  iya 'kifar da ita shine ta fito da dukkan ƙarfin ta tare da goyon bayan Amurka da wasu Shuwagabannin Yankin Tekun fasha inda sai suka Murƙushe masu yunkurin.   Dakarun Saddam sunyi kisa na rashin tausayi babu kakkautawa, sannan suka rugurguza Da yawa daga cikin Gine ginen Haramin mai tsarki.

abubuwan da aka makala