Sashen Ayyukan Injiniyanci na Ataba Hussainiya ta sanar da ci gaba da gudanar da aikin Fadada Farfajiyan Zainab Aqeelah tare da bayyana adadin da aka kammala na ayyukan yanzu.

Sashen koyar da ayyukan Injiniyanci da fasaha na Hubbaren Imam Husain {as} ya sanar da ci gaba da gudanar d ayyukan Haramin na farfajiyan Zainab Aqila {as} acikin ci gaba da fadada .

Hubbaren Imam Husain {as}, ta bayyana adadin nasorin da ta samu aciki aikin

shugaban sashen Injiya Husain Rida Mahdi ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan yanar gizo cewa , masu aikin injiniyanci da fasaha na sashin mu naci gaba da gudanar da aiki a farfajiyan Zainab Aqila Aminci Allah ya tabbata a gareta wanda shine kashi na farko na fadada Hubbaren Imam Husain {as}

ya bayyana cewa kammala aikin yakai kashi Hamsin da biyar cikin dari ,kuma ana ci gaba da aikin sannan anaso a kammala shi acikin shekara mai zuwa.

ya kara da cewa ayyukan kanikanci da na lantarki da Na'urorin daukan hoto dana kashe wuta baya ga wasu ayyuka ana gudanar da su ne bisa wasu tsare tsare na musamman, kuma yayi nuni da cewa aikin farfaajiyan na zainab Aqila na daya daga cikin muhimman ayyuka na fadada Marqadin Imam Husain , wacce Ataba Husainiyya tasa a gaba kuma yankin aikin yakai murabba'in mita dubu 152. wanda aciki kamar yadda aka tsara akwai hade shi da Tal'abu zainab da dakin magani da wuraren sabis

Abin lura shine ita Haramin Imam Husain ta sanar da kammala dukkan ayyukan da suka shafi siminti a ranar 12 ga sha'aban wacce tayi daidai da 16 ga maris 2022 .

haka kuma hukumar gudanarwa sashen ta bullo da wani shiri na bude bangaren hidima da zasu kasance a Hidimar Maziyarta yayin ziyaran miliyoyin mutane a taron Arba,enn

Tarja

Sayyid Adam Jubulwa

abubuwan da aka makala