Sanya Sunan ka da wanda kake so domin yi maka ziyarar Imam Husain [as] maimakon ka a Daren da yafi dare dubu Alkhairi

Mu'assatul Imam Husain (as) Bangaren yada labarai ta yanar Gizo Karkashin Haramin Imam Husain tana Mai sanar da ku daukar nauyin yi muku ziyarar Imam Husain (as) a Daren Lailatul Qadari na uku kuma na karshe a madadin ku da sunaye da kuka saka domin sanya sunan ka da Wanda kake so shiga wannan link din dake kasa

https://www.imamhussain.org/hausa/enaba

Shugaban sashin wala Assafari yana cewa Bangaren sharifai masu Hidiman Harami hadin guiwa da wanann mu'assa za su gudanar Imam Husain (as) na Daren Lailatul kadari karshe Ga dukkan wadanda suka sanya sunayen su a wannan shafin namu na Haramin Imam Husain

 Yayi nuni da cewa ruwayoyin da Dama na Ahlul bait (as) da sukayi nuna Akan falalar Ziyaran Imam Husain (as) a wannan Daren, wacce take da falala Mai yawan gaske

Sannan zamu rufe karban sunaye ne ranar 24/04/2022 da Misali karfe 7:00 na yamma

 Ya Ci gaba da cewa ko wana mutum zai iya aikowa da sunaye marasa iyaka

abubuwan da aka makala