Ci gaba da taron karatun Qur'ani da Muhadarori hadi da raya Bukukuwa na Ahlul bait a Nahiyar Afrika karkashin Haramin Harami Imam Husain (as)

Mu’assasa Warisil Anbiya (as) da ke da alaka da sashin kula da harkokin addini a Hubbaren Imam Husain , na ci gaba da gudanar da tarukan kur’ani, da ayyuka, da laccoci, da tunawa da bukukuwa na Haihuwar Ahlul-Baiti. Bayt (as) a nahiyar Afirka.

Jagoran sashin ayyukan Afirka a sashe Harami , Sheikh Ali Qar’awi, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da shafin yanar gizo , inda yake cewa, Haramin Imam Hussain yana ci gaba da gudanar, da cibiyoyin da ke da alaka da shi a kasashen duniya, musamman ma a kasashen Nahiyan. Afirka, don yada ilimin Ahlul Baiti amincin Allah ya tabbata a gare su ta hanyar shirya tarukan addini da wayar da kai da zamantakewa, a ita Nahiyya Africa 

Ya bayyana cewa: ita Haramin Imam Hussain tana da cibiyoyi da dama da suka yi rajista a cikin ta kamar (Burkina Faso, Uganda, Mali, koddebuwa da Liberia) wadannan cibiyoyi na ci gaba da raya bukukuwa na Haihuwar Ahul bayt da ranakun wafatin su 

Ya kara da cewa Harami Imam Hussain ta kawwana wasu muballigai da suka kammala karatun Hauza a Kasar Iraki a karkashin kulawar ta wanda ta dauki nauyin karatun su tare da kaddamar mu su da abubuwan bukatun su acikin Iraki sannan kuma ta maida su gida bayan kammala karatun domin ci gaba da isar da sakon Ahlul bait (as) a Nahiyan su 

Ya kara da cewa, kungiyar ta bullo da wani shiri nan gaba na fadada ayyuka a Nahiyar Afirka ga dimbin mabiya Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su), tare da bude cibiyoyin addini, da makarantu . a wasu kasashe bayan kammala ayyukan rajista a hukumance."

Wani abin lura shi ne sashin kula da harkokin addini na sashin kula da ayyukan jama'a a hubbaren Imam Husain ya himmantu matuka da daukar nauyin makarantu da cibiyoyi da dama da suke a ciki da wajen kasar Iraki, kuma suna da himma wajen samar da hidimomi da tallafin da suka wajaba ga dalibansu. da kuma bibiyar ayyukan wadannan makarantu da cibiyoyin

 Tarjam

Sayyid Adam Jubulwa