Ma'aikatar kimiya da Fasaha na Haramin Imam Hussaini (as) tana sanar da bude asibitin koyarwa na masu kula da mata masu juna biyu a Asibitin mata na Al-Batool, Al-Shifa (19) wanda ke daura da birnin Mosul,
Shugaban sashen Injiniya Hussein Rida Mahdi, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan yanar gizon ya ce, “a halin yanzu ’yan kungiyar mu suna ci gaba da gudanar da aikin gine-gine a asibitin Al-Shifa mai lamba 19 (mustashfal Albatul )a gefen dama." ga birnin musul
Ya bayyana cewa, kammala wannan aikin ya kai kashi casa’in da bakwai (97%), kuma asibitin yana da gadaje (220), da filin gini na murabba’in mita 7000, kuma ana sa ran bude shi a watan Fabrairu mai zuwa. ."
Ya kara da cewa, “Wannan aikin yana da tsada kuma Haramin Imam Husain (as) ne ke daukar nauyin ayyukan
Sannan da zarar kammala aikin ita Haramin zata gudanar da Asibitin ga masana jinya
Sannan zai kasance jinyar kyauta ne ga daukacin ‘yan kasa bayan an mika shi gaba daya ga sashin kula da lafiya na Harami
Kamar yadda aka sanya shi a cikin jerin cibiyoyin warkarwa a matsayin tallafi. kokarin da jami'an kiwon lafiya ke yi a dukkan jahohin kasar Iraki kenan
An bayyana cewa Haramin Imam Hussaini ta hanyar fassara umarnin wakilin ma’aikatar lafiya da kuma limamin Harmin Sheikh Abdul Mahdi al-Karbalai, yana aiwatar da ayyukan hidima da dama, na musamman a bangaren kiwon lafiya, kuma yana aiki don ba da dama na jinya ga 'yan ƙasa, musamman ma iyalan shahidai, marasa galihu, da masu ƙarancin kuɗi. kyauta.
Tarjama
Sayyid Adam Njubulwa
اترك تعليق