A karkashin kulawar Haramin Imam Husain (as) da hadin guiwa Dandalin matasa an gudanar da taron yaye Daliban Jami'ar Waris dake karkashin haramin Imam husain
Mataimakin Shugaban Jami'ar Dr Abbas Al_Daami ya bayyana a wata hira da yayi da Shafin yanar Gizon Hukuma cewa: Jami'ar ta gudanar da taron yaye Daliban ne a babban dakin taro dake cikin Hubbaren Imam Husain (as) kuma wannan taron shine karo na farko da aka yaye Daliban Jami'ar
Yaci gaba da cewa bikin tazo da salo kala kala sannan ofishin Jami'ar ta bayar da kyauta ga dukkan Daliban da aka yaye daga bisani kuma sukaje jikin Hubbaren Imam Husain domin yin rantsuwa da cewa zasuyi aiki na jin kai ga Al'umma da yada Ilimi da Iklasi da kuma isar da sakon Gidan manzo Allah (saw)
Ya kuma kara da cewa duk Wanda aka yaye za'a dauke su aiki a sassan wurare na ma'aikatan Haramin Imam Husain Aminci Allah ya tabbata a gare Shi
Yana da kyau a lura cewa Harami Imam husain ta bude jami'ar ne a shekaran karatu na (2017_2018) Wanda ya hada da bangarori kamar su karatun kiwon Lafiya, Injiniya, tattalin Arziki da kuma Ilimin musulunci
Tarjama
Sayyid Adam NJubulwa
اترك تعليق