An gudanar da Jana'izar Babban Malamin Addini Sayyid Muhammad Sa'idul Hakim a Haramin Imam Husain (as)

A cikin wani yanayi na bakin ciki, haramin Imam Husaini, amincin Allah ya tabbata a gareshi ta gudanar da Jana'iza a safiyar yau Asabar (4/9/2021), na babban malamin Addini, Sayyid Muhammad Saeed Al- Hakim Allah ya jikan sa

 Shugaban sashin watsa labarai na Haramin Imam din, Aqeel Al-Sharifi, a cikin jawabinsa ga gidan yanar gizon hukuma yace "Haramin Imam mai tsarki ya karbi gawar marigayi babban malamin addini, Sayyid Muhammad Saeed Al-Hakim Allah ya jikan sa , kuma an yi bukukuwan jana'iza a haramin Imam Al-Husaini (a.s). "

 Ya kara da cewa "wakilin babban malamin addini, Sheikh Abdul-Mahdi Al-Karbalai, da wasu Jami'ai na Haramin Imam Hussain, sun karbi akwatin gawar marigayin, kuma sun yi ma sa ziyarar Imam Husaini (a.s). kafin a yi masa fareti an kewayen haramin Imam Husaini (as) da gawar Malamin a cikin Wuri Mai Tsarki, tare da halartar dimbin Jama'ar manzo (saw)

 Ya yi nuni da cewa "manyan sakatarori guda biyu na haramin Imam Husain da na Abdul Fadal , suna juyayin rasuwar babban malamin Addini, Sayyid Muhammad Saeed Al-Hakim yana mai nuni da cewa"  An bawa Harami gawar Malamin a jiya, Juma'a, 

Muna ma su cewa (Inna lillahi wa ilaihirraji'un)

. Manyan sakatarori guda biyu na wuraren ibada biyu masu tsarki, Husainiyya da Abbasiyya, suna juyayin Rashin Babban Ayatollah, Sayyid Muhammad Saeed Al-Hakim suna ma su cewa Allah ta'ala ya hada Shi da manzo Rahma Muhamamd (saw), sanan su na mika ta'aziyyar su ga mai shekaru da lokaci, da fatan Allah ya gaggauta bayyanarsa (AF), kuma suna mika Ta'aziyar su ga Maraji'an mu ma su girma , da al'ummar musulmai gaba daya , su na rokon Allah Madaukakin Sarki da ya hada shi da kakansa, Manzon Allah da Iyalan gidan sa tsarkaka

 Yana da kyeu mutane su san tarihin shi marigayin, shine Sayyid Muhammad Saeed, ɗan Ayatullah Sayyid Muhammad Ali bin Sayyid Ahmed bin Sayed Mohsen bin Sayed Ahmed bin Sayed Mahmoud bin Sayyid Ibrahim (likitan), ɗan Yarima Sayyid Ali al-Hakim, ɗan Yarima Sayyid Murad al -Tabataba'i, ya hau zuwa zuriya mai daraja ga Ibrahim Tabataba bin Ismail al-Dibaj. Bin Ibrahim Al-Ghamr Bin Al-Hassan Al-Muthanna Bin Al-Imam Al-Hassan Bin Ali Bin Abi Talib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), an haife shi a garin Najaf Al-Ashraf, a ranar takwas ga watan zulqada 1354 AH daidai da 1936 , kuma ya rasu bayan bugun zuciya kwatsam a ranar 25 ga Muharram don tunawa da Shahada. na Imam Ali bin Al-Hussein Al-Sajjad (a.s)

Tarjama

Sayyid Adam Jubulwa

abubuwan da aka makala