Wakilin Babban Malamin Addinin Iraq har wa yau kuma mai Jiɓintar Al'amurar Shari'a na Haramin Imam Husain (as) Shaikh Abdul Mahdi Limamin Haramin Imam Husain yayi Rangadin don duba Irin Ayyukan da Mu'assasar Waris na ƙasa da ƙasa ta gabatar ga Marasa lafiya cikin ƙasa da wata guda da bude ta.
Shugaban sashen Tiyata na cutar daji a Asibitin, Dakta Nawfal Shadud ya ce; Mu'assasar tana farin ciki da Ziyarar da Wakilin babban Marji'i Addini kuma limamin Haramin Imam husain (as) Shaik Abdul-mahdi ya kawo mata da nufin yin dubi da bitar ayyukan likitanci da Haramin ta bayar, da kuma saduwa da yayi da marasa lafiyan da ke cikin Asibitin .
Inda Ya ƙara bayyana cewa;
"Abu ne mai kyau samun gamsuwar marasa lafiya da ayyukan da ake gabatarwa"
Ya kara da cewa ziyarar Sheik Al-karbala'i ta zo ne da nufin hanzarta shawo kan matsalolin da ake fuskanta, kuma da yardar Allah babu wani cikas, sannan ya gudanar da Taro da ma'aikan lafiya da na fasaha a cibiyar, injiniyanci da kuma wakilai na bangarori.
Babban Malamin Shaikh Abdul Mahdi ya tabbatar cewa Haramomi fa ba suna zamo madadin Gwamnati bane ko kuma wani bangare na Hukuma ta hanyar Ayyukan su da sukeyi da kula da marasa lafiya da bada karatu, a 'a su suna so ne su zama ma su taimakawa Gwamnati ne wajen Hidimtawa Al'umma.
اترك تعليق