Harami Imam Husain Mai Alfarma ta sanar da cigaba da aikin ginin Jami'atuz-Zahra (as) wanda Haramin ke ginawa ga mata zallah a Garin Karbala, shi dai wannan jami'a shine nau'insa na farko a kasar Iraki Wanda ana fatan bude makarantan zuwa makon karatu na gaba. Manajan aiki Injiya Hussam Abdul Hadi,ya fada a wata Hira da gidan Yanar gizon Hukuma cewa Injiniyoyi da kuma masu kula da fannin fasaha na Haramin ne ke kula da aikin ginin na Jami'ar Azzahra kuma izuwa yanzu aikin yakai kaso (85%). Ana fatan aikin zai kammalu kuma a bude Shi a shekara mai zuwa. Ya bayyana cewa aikin yana ɗaya daga cikin mahimman ayyuka kuma ana aiwatar da shi ne bisa ga tsarin gine_ gine na zamani kamar yadda kayan da ake amfani da su wajen cimma gini ɗin duk ingantattu ne irin na ƙasa da ƙasa. Ya kara da cewa Jami'ar ta hada da kwalejin kimiyyar magunguna,kiwon lafiya, da kuma hadi da kwalejin larabci (Turanci da lissafi) . Yayi nuni da cewa aikin ya hada da gine-gine da dama, aciki har da manya da wasu sassa daban daban . Abin lura a nan Shi ne ita Haramin Imam Husain mai mai Alfarma, ta hanyar Shiryayrwar Wakilin babban Marji'i a Haramin Shaik Abdul Mahdi Karbala'i tana yin ayyuka na bangarori da dama don amfanar Al'umma.
اترك تعليق